Neuer zai yi jinya zuwa watan Janairu

Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Neuer ya karya kafa a cikin watan Afirilu

Mai tsaron ragar tawagar kwallon kafar Jamus da Bayern Munich, Manuel Neuer zai yi jinyar raunin da ya yi a kafarsa ta hagu zuwa watan Janairun 2018.

Dan wasan mai shekara 31, ya yi irin wannan raunin a kafarsa ta hagu a watan Afirilu, yanzu kuma ya fama ciwon a lokacin atisaye a ranar Litinin.

Bayern tana rukuni daya da Celtic a gasar cin kofin Zakarun Turai, kuma Neuer ba zai buga wa kungiyar sauran wasannin cikin rukuni biyar ba.

Yanzu haka Sven Ulreich mai shekara 29 ne zai maye gurbinsa, wanda ya buga wasa 12 a Munich din tun lokacin da ya koma can da murza-leda daga Stuttgart.

Munich wacce ta ci Andelecht a wasan farko a cikin rukuni za ta ziyarci Paris St-Germain, sannan ta karbi bakuncin Celtic a ranar 18 ga watan Oktoba.