Rio Ferdinand zai koma damben boksin

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ferdinand tsohon dan wasan tawagar kwallon kafa Ingila da Manchester United

Tsohon kyaftin din Manchester United, Rio Ferdinand zai koma wasan damben boksin bayan shekara biyu da ya yi ritaya daga buga tamaula.

Wani kamfanin caca mai suna Betfair ne ya yi ruwa da tsaki na ganin Ferdinand mai shekara 38 ya shiga boksin, kuma shi ne ya sanar da amincewar dan wasan a ranar Talata.

Ferdinand tsohon dan wasan tawagar kwallon Ingila yana aiki a matsayin mai sharhi da bayanan wasanni yana kuma da kamfanin kayayyakin sawa.

Dan wasan wanda ya ci kofin Premier shida da na Zakarun Turai daya a lokacin da ya murza-leda a United ya bi sahun tsohon dan wasan Birmingham, Curtis Woodhouse da tsohon dan kwallon Crystal Place, Leon McKenzie wadan da suka shiga boksin bayan buga tamaula.