Ronaldo zai dawo buga gasar La Liga

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ronaldo ya ci kwallo 286 a wasa 265 da ya yi a gasar La Liga

Cristiano Ronaldo zai dawo buga wa Real Madrid wasan farko a gasar La Liga ta bana a ranar Laraba, bayan da ya kammala hukuncin dakatar da shi wasa biyar da aka yi.

An dakatar da Ronaldo buga wasa biyar, bayan da aka ba shi jan kati a karawar da Real Madrid ta ci Barcelona 3-1 a Spanish Super Cup.

Cikin wasa biyar din Ronaldo bai buga karawa da Barcelona a gasar Spanish Super Cup da Deportivo La Coruna da Valencia da Levante da kuma Real Sociedad duk a wasan La Liga ba.

Ronaldo ya ci kwallo uku a kakar bana a European Super Cup da Spanish Super Cup da wanda ya ci Apoel a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Real Madrid za ta kara da Real Betis a wasan mako na biyar a gasar La Liga a ranar Laraba.