'A daina yi wa Romelu Lukaku wakar wariya'

Manchester United striker Romelu Lukaku

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Lukaku ya ci wa Manchester United kwallaye 5 cikin wasanni biyu a wannan kakar

Wata kungiyar da ke fafatukar hana wariya, Kick It Out, ta bukaci kungiyar Manchester United da ta hana magoya bayanta rera wake-waken wariya ga Romelu Lukaku.

Kungiyar ta ce wakar, wadda a cikinta ake kalamai kan girman mazakutar dan wasan gaban kasar Belgium din, nuna wariya ce.

"Babu yadda za a lamunci nuna wariya, ko da kuwa hakan na nufin nuna goyon baya ne ga dan wasa," in ji kungiyar Kick It Out.

Manchester United ta ce za ta tattauna da kungiyar Kick it Out game da lamarin.

Kungiyar kwallon kafar tana jiran samun tabbaci kan ko rera wakokin za su iya kasance laifin da za a iya gurfanar da mutum a gaban kotu.