Ba ni da hannu a daukar nauyin IPOB — Jonathan

Goodluck Jonathan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mista Jonathan ya soki gwamantin Buhari da mayar da hankali kan yada farfaganda maimakon aikin gwamnati

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce ikirarin da ministan yada labaran kasar, Lai Mohammed, ya yi cewar 'yan hamayya ne ke daukar nauyin kungiyar masu fafatukar kafa kasar Biafra ta IPOB ya nuna cewar har yanzu gwamnatin Buhari na ci gaba da yada farfaganda maimakon mayar da hankali kan aiki.

A wata sanarwar da Reno Omokri, mataimaki na musamman kan shafukan sadarwar zamani ga Shugaba Goodluck Jonathan, ya wallafa a shafin Facebook na tsohon shugaban kasar, cewa idan gwamnatin Najeriya ta san 'yan hamayyar da ke daukar nauyin 'yan IPOB, ta kama su tare da gurfanar da su gaban kotu.

Mista Jonathan ya ce bai dace a yi amfani da soji wajen dakile laifuka a cikin gida ba, domin an ba su horarwar yakar abokan gabar kasa da ke waje ne.

Ya ce maimakon soji, 'yan sanda ne ya kamata a yi amfani da su wajen kwantar da tarzomar cikin kasa.

Tsohon shugaban Najeriyar ya kara da cewar, idan sojoji suka fara yi wa fararen hula barazana, to maimakon a kwantar da tarzoma sai hakan ya zama barazana ga mutane.

A shekarar 2015 ne Mista Goodluck Jonathan ya mika mulki ga Shugaba Buhari bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar a shekarar.