Scotland ta raba-gari da kocinta Gordon Strachan

Hakkin mallakar hoto SNS
Image caption Scotland ta raba-gari da Gordon Strachan

Gordon Strachan ya bar mukaminsa na kocin Scotland bayan da suka cimma matsayar amincewa tsakaninshi da kungiyar.

An yanke shawarar ne tare da hadin gwiwar hukumar kwallon kafa ta Ingila, bayan da kasar ta kasa zuwa manyan wasannin kasa-da-kasa guda biyu a jere.

Strachan da mataimakinsa Mark McGhee sun sauka daga mukamin ba tare da bata lokaci ba.

"A madadin hukumar ina mika godiya ga Gordon a kan jajircewarsa a kungiyar". In ji shugaban hukumar Stewart Regan.

A watan Janairun 2013 ne aka nada Strachan a matsayin kocin kungiyar, wanda ya maye gurbin Craig Levein a matsayin wanda zai taka rawa da kuma sa ido a wasan neman shiga gasar duniya ta 2014.

Labarai masu alaka