Guardiola ya raina mana wayo – Pochettino

A gobe Asabar ne Tottenham za ta karbi bakuncin Bournemouth a Wembley.
Image caption A gobe Asabar ne Tottenham za ta karbi bakuncin Bournemouth a filin wasa Wembley

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce, maganganun da Pep Guardiola ya yi na cewa kungiyar ta dogara ne a kan Harry Kane "rainin wayo ne".

Kocin Mancherster City ya bayyana kungiyar a matsayin "kungiyar Harry Kane", yayin da yake magana a kan abokiyar hamayyarsa.

Dan kwallon ya ci kwallo 11 a wasa bakwai da kungiyar ta buga a bana.

Pochettino ya kara da cewa: "Guardiola na cikin wadanda suka kawo nasara a Barcelona kuma ban taba cewa kungiyar Lionel Messi ba ce."

A gobe Asabar ne Tottenham za ta karbi bakuncin Bournemouth a filin wasa Wembley.

Labarai masu alaka