U-17: Nijar ta kai zagayen gaba

Niger and South Korea Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wannan ne karon farko da Nijar ta samu shiga gasar duniya

Nijar ta kai matakin zagaye na gaba a gasar cin kofin duniya da ake yi a Indiya na 'yan kasa da shekara 17, yayin da aka yi waje da Guinea daga gasar.

Nijar ta kai matakin inda ta kafa tarihi a shiga gasar duniya, wanda ba ta taba samun wannan damar ba a tarihi.

Duk da rashin nasarar da Nijar ta yi a hannun Brazil da ci 2-0 a wasansu na karshe a rukunin D, Nijar ta matsa gaba ne saboda tana cikin kasahen da suka nuna bajinta a gasar.

Ita ma kasar Jamus ta doke Guinea da ci 3-1 a rukunin C.

Labarai masu alaka

Karin bayani