Zinedine Zidane ya jinjina wa Harry Kane

Zinedine Zidane says Harry Kane is a complete player Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsohon dan wasan tsakiyar Real Madrid da Juventus da kuma Faransa, Zinedine Zidane ya ksance daya daga cikin gwanayen 'yan wasa a zamanin da yake taka leda

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane, ya bayyana dan wasan Tottenham, Harry Kane, a matsayin cikakken dan wasa kafin kungiyoyin wasan biyu su hadu a wasan gasar zakarun Turai ranar Talata.

Amman Zidane ya ki ya yi tsokaci kan ko zakarun Spaniyan za su sayi dan wasan gaban mai shekara 24.

Dan wasan Ingilan ya ci kwallaye 43 a wasanni 38 ga kungiyar kwallon kafarsa da kuma kasarsa a shekarar 2017.

"Yana da kyau ta ko ina, kuma ko da yaushe yana tunanin cin kwallo ne cikin ko wanne hali ," in ji Zidane, mai shekara 45.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba