'Yan Madrid 19 da za su kara da Tottenham

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real ce mai kofin Zakarun Turai har guda 12 jumulla

Real Madrid za ta karbi bakuncin Tottenham a gasar cin Kofin Zakarun Turai fafatawar cikin rukuni na takwas a Bernabeu a ranar Talata.

Real da Tottenham sun kara a baya a wasannin cin kofin zakarun Turai sau hudu, kuma Real ta yi nasara a fafatawa uku.

Madrid da Tottenham sune ke kan gaba a teburin rukuni na takwas da maki shida-shida, sai Borussia Dortmund da Apoel Nicosia.

Ga jerin 'yan wasan da za su fuskanci Tottenham

Masu tsaron raga: Navas, Casilla and Moha.

Masu tsaron baya: Ramos, Varane, Nacho, Marcelo, Theo and Achraf.

Masu wasan tsakiya: Kroos, Modric, Casemiro, Llorente, Asensio, Isco and Ceballos.

Masu cin kwallo: Cristiano Ronaldo, Benzema and Lucas Vázquez.

Labarai masu alaka