Leicester ta raba gari da koci Shakespeare

Leicester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan Yuni Shakespeare ya karbi aikin rikon kwarya a Leicester City

Leicester City ta sallami kocinta Craig Shakespeare wata hudu bayan da ya saka hannu kan yarjejeniyar jan ragamar kungiyar shekara uku.

Shakespeare mai shekara 53, ya maye gurbin Claudio Ranieri a watan Fabrairu, wanda kungiyar ta kora bayan da ya kasa taka rawar gani.

Bayan da Shakespeare ya tsallakar da Leicester daga hadarin barin gasar Premier a bara ne inda kungiyar ta yi ta 12 a kan teburin gasar ya sa aka ba shi aiki a watan Yuni.

Leicester City tana ta 18 a kan teburin Premier bana, kuma ba ta ci wasa ba a karawa shida da ta yi a jere, bayan da aka buga fafatawar mako takwas a gasar.

Kocin ya ci wasa takwas daga 16 da ya ja ragamar kungiyar a bara, sannan ya kai ta wasan daf da na kusa da karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai wacce Real Madrid ta lashe.

Labarai masu alaka