An zargi Marcelo da kin biyan haraji

Real Madrid Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun a shekarar 2013 mahukuntan Spaniya suka fara binciken Marcelo

Mahukunta a Spaniya sun zargi dan kwallon Real Madrid Marcelo da kin biyan haraji da ya kai kudi fam 436,000.

Masu shigar da kara sun alakanta rashin bin ka'ida da dan kwallon ya yi ta hanyar bude kamfani a waje da yake kula da kudin da yake samu ta fuskar tallace-tallace.

Har yanzu dai Marcelo mai shekara 29 dan kwallon tawagar Brazil, bai ce komai ba dangane da zargin da ake masa.

Shi ne dan wasa na baya-bayan nan da mahukuntan Spaniya ke zargi da kaucewa biyan haraji, bayan Messi da Neymar da Ronaldo.

Lamarin ya faro ne tun daga shekarar 2013.

Labarai masu alaka