Napoli ba kanwar lasa ba ce - Pep Guardiola

Manchester city beats Napoli 2-1 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester City ta doke Napol 2-1

Duk da cewar Manchester City ta doke kungiyar kwallon kafa ta Napoli 2-1 a Etihad ranar Talata a fafatawar da suka yi a wani wasan gasar zakarun Turai, kociya Pep Guardiola ya ce kungiyar ta Napoli ba kanwar lasa ba ce.

Guardiola ya jinjina wa kungiyar kwallon kafar da ke taka leda a gasar Serie A.

"Na sani kafin mu yi wasa da kuma bayan mun yi wasan cewa Napoli daya ce daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai," in ji Guardiola.

Ya kara da cewa: "Karawar da muka yi da su daya ce daga cikin fitattun wasanni.

"Na san kungiyar da muka doke. Kungiyoyin da suka kai matakinta ba cikin sauki ake doke su ba."

Watakila Mourinho ya koma Faransa da koci

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pep Guardiola ya ce: "Karawar da muka yi da su daya ce daga cikin fitattun wasanni."

Labarai masu alaka