Senegal ta gayyaci Mane mai jinya

Senegal
Image caption Kocin Senegal ya ce yana fatan Mane zai warke kafin fafatawar da za su yi da Afirka ta Kudu

Tawagar kwallon kafa ta Senegal ta gayyaci Sadio Mane domin ya buga mata wasan shiga gasar cin kofin duniya a watan gobe, duk da jinyar da yake yi.

Dan kwallon ya yi rauni ne a lokacin da ya buga wa Senegal wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka kece raini da Cape Verde.

Senegal za ta kara da Afirka ta Kudu a wasan da za su yi gida da waje, inda fafatawar farko za suyi ne a ranar 10 ga watan Nuwamba, sannan wasa na biyu ranar 14 ga watan.

A ranar 10 ga watan Oktoba Liverpool ta tabbatar da cewar Mane zai yi jinyar mako shida.

Ba a tabbacin ranar da Mane zai dawo fagen murza-leda kuma tuni Liverpool ta kara da Manchester United da Maribor ba tare da dan kwallon ba.

Labarai masu alaka