Messi ya ci kwallo 100 a wasannin nahiyar Turai

Champions League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ta hada maki tara a wasa uku da ta buga

Lionel Messi ya ci kwallo na 100 a wasannin nahiyar Turai, bayan da Barcelona ta ci Olympiakos 3-1 a gasar Zakarun Turai a ranar Laraba a Nou Camp.

Barcelona ta fara cin kwallo a minti na 18 da fara tamaula bayan da Dimitris Nikolaou ya ci gida.

Bayan da aka dawo ne Lionel Messi ya kara ta biyu sannan Lucas Digne ya kara na uku, sai dai kungiyar ta kammala karawar da yan wasa 10 a fili bayan da aka bai wa Pique jan kati.

Sai dai kuma daf da za a tashi daga karawar Olympiakos ta zare kwallo daya ta hannun Dimitris Nikolaou.

Daya wasan na rukuni hudu kuwa Juventus ce ta doke Sporting da ci 2-1.

Da wannan sakamakon Barcelona ta hada maki tara sai Juventus da maki shida sai Sporting da maki uku sannan Olympiokos ta karshe wacce ba ta da maki.

Labarai masu alaka