Chelsea da Roma sun ci kwallo shida tsakaninsu

Champions League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kwallo biyun da Hazard ya ci sune na farko da ya ci wa Chelsea a bana

Karawar da aka yi tsakanin Chelsea da Roma a gasar cin kofin Zakarun Turai sun tashi 3-3 a fafatawar da suka yi a Stamford Bridge a ranar Laraba.

David Luiz ne ya fara ci wa Chelsea kwallo, sai kuma Eden Hazard da ya ci biyu rigis a karawar.

Ita kuwa Roma ta fara cin kwallo ta hannun Aleksandar Kolarov daga baya shi ma Edin Dzeko ya ci biyu a fafatawar.

Daya wasan rukuni na ukun tsakanin Qarabag da Atletico Madrid tashi suka yi babu ci.

Chelsea ce ta daya a rukuni na ukun da maki bakwai, sai Roma da maki biyar, Atletico maki biyu ne da ita da kuma Qarabag mai maki daya kacal.

Labarai masu alaka