Man United ta yi wasa 12 a jere ba a doke ta ba

Champions League Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasa nma 12 da Manchester United ta yi a jere ba a doke ta ba

Manchester United ta ci Benfica daya mai ban haushi a gasar cin kofin Zakarun Turai da suka kara a Portugal a ranar Laraba.

Marcus Rashford ne ya ci kwallon a bugun tazara, bayan da mai tsaron raga ya kama tamaular a cikin ragar.

Da wannan sakamon United ta yi wasa 12 a jere ba tare da an doke ta ba, tun fara kakar kwallon kafa ta shekarar nana.

Cikin wasa 12 da ta buga ta ci 10 sannan ta yi canjaras a fafatawa biyu, daga ciki ta buga Premier takwas da wasa a kofin Zakarun Turai sau uku da karawa a League Cup.

United za ta ziyarci Huddersfield a wasan mako na tara a gasar cin kofin Premier a ranar 21 ga watan Oktoba.

Labarai masu alaka