Ban ga laifin tsare bayanmu ba - Jose Mourinho

Mile Svilar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mile Svilar ya kusa yin hawaye a karshen wasan. Dan uwansa na kasar Bejium, Romelu Lukaku ya je ra rarrashe shi.

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce babu laifi in kungiyarsa ta kware a tsaron baya, bayan United ta doke Benfica 1-0.

Marcus Rashford ne ya ci kwallo dayan da aka ci a wasan a lokacin da ya yi bugun tazara wadda ta zo wa sabon mai tsaron gida, Mile Svilar, da bazata.

An soki United kan salon wasan da ta yi a kece-rainin da suka tashi 0-0 da Liverpool ranar Asabar inda suka auna mai tsaron gida sau daya tak, amman an ci Red Devils kwallo shida ne kawai a kakar bana.

"Mu ne muke da karfin guiwa kuma mu ne muka juya akalar wasan," in ji tsohon kocin Benfica Mourinho. "Ban taba tunanin cewa za a iya cinmu ko kwallo daya ba, mun tsare baya.

"A wasu lokutan sai in ji kwarewa a tsaron baya wani laifi ne, amman ba laifi ba ne. Kwarewa a tsaron baya wani mataki ne na samun sakamako mai kyau. Mun san matsin Benfica ba zai kai miniti 90 ba.

"Irin tsare bayan da Liverpool ta yi a wasanmu da su, Benfica ta gaza yin hakan zuwa karshen wasa. Ko babu matsi, mun san za mu ci kwallo."

Labarai masu alaka