Messi ne gwarzon dan wasa – Valverde

Messi ya ci kwallo na 100 a wasannin nahiyar Turai
Image caption Messi ya ci kwallo na 100 a wasannin nahiyar Turai

Kocin Barcelona Ernesto Valverde, ya ce Lionel Messi zai ci gaba da amsa sunansa na fitaccen dan wasa a duniya ko ya lashe kyautar Ballon ta bana ko bai lashe ba.

A farkon watan nan ne mujallar kwallon kafa ta Faransa ta fitar da sunayen fitatttun 'yan wasan, inda mutane da dama suka yi amannar cewa Cristiano Ronaldo na Real Madrid zai iya lashe kyautar.

Ko da yake kocin ya gamsu cewa Messi ba ya bukatar wata kyauta da za ta nuna shi ne fitaccen dan wasa a duniya.

A ranar Laraba ne Lionel Messi ya ci kwallo ta 100 a wasannin nahiyar Turai, bayan da Barcelona ta ci Olympiakos 3-1 a gasar Zakarun Turai a Nou Camp.

Labarai masu alaka