Fifa U17: Mali ta fitar da Ghana

FIFA U17 Hakkin mallakar hoto FIFA
Image caption Mali za ta buga wasan daf da karshe da Iran ko Spaniya a ranar Laraba

Tawagar kwallon kafar Mali ta kai wasan daf da karshe bayan da ta ci ta Ghana 2-1 a gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan shekara 17 da ake yi a India.

Mali ce ta fara cin kwallo ta hannun Hadji Drame a fafatawar da suka yi a filin wasa na Gandhi Athletic da ke Guwahati a ranar Asabar.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Mali ta kara ta biyu ta hannun Djemoussa Traore, saura minti 20 a tashi Ghana ta zare kwallo daya ta hannun Kudus Mohammed a bugun fenariti.

Mali za ta buga wasan daf da karshe tsakanin Spaniya ko Iran a filin wasa na Navi da ke Mumbai a ranar Laraba.

Labarai masu alaka