''Ozil bai damu da batun komawa United ba''

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Karshen kakar nan yarjejeniyar Ozil za ta kare a Arsenal

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce Mesut Ozil bai damu da rade-radin da ake cewar zai koma Manchester United da murza-leda ba.

Wenger ya ce Ozil dan wasan tawagar Jamus ya maida hankali ne wajen buga wa Arsenal wasanni bai taba barin jita-jitar ta tayar masa da hankali ba.

A karshen kakar bana yarjejeniyar Ozil za ta kare a Arsenal, kuma har yanzu bai saka hannu kan tsawaita zamansa a kungiyar ba, duk da tuntubarsa da Gunners ta dinga yi.

Dan kwallon mai shekara 29 baya kan ganiyarsa, shi ya sa ake cewar zai koma Manchester United a watan Janairu.

Ozil ya yi aiki tare da Jose Mourinho a Real Madrid kafin daga baya ya koma Arsenal da taka-leda.

Labarai masu alaka