Man City ta bayar da tazarar maki biyar

Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sergio Aguero ya ci wa City kwallo na 177 a bugun fenariti

Kungiyar Manchester City ta bai wa Manchester United tazarar maki biyar, ta kuma ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier, bayan da ta ci Burnley 3-0 a ranar Asabar.

City ta fara cin kwallo ta hannun Sergio Aguero a bugun fenariti, kuma na 177 da ya ci wa City tun komawarsa can da taka-leda.

Hakan ne ya sa ya yi kan-kan-kan da Erik Brook wanda tun farko ya ci 177 tsakanin 1928 zuwa 1939 a kungiyar ta Ettihad.

Daga baya ne Nicolas Otamendi da kuma Leroy Sane suka ci wa City sauran kwallayen da suka bai wa kungiyar damar hada maki uku rigis a fafatawar.

City ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier da maki 25, yayin da Manchester United wacce Huddesfield ta doke ta 2-1 ke ta biyu da maki 20.

Labarai masu alaka