Arsenal ta koma ta biyar a teburin Premier

Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal ta ci kwallo 17 an kuma zura mata 12 a wasannin Premier bana

Kungiyar Arsenal ta koma mataki na biyar a kan teburin Premier, bayan da ta ci Everton 5-2 a wasan mako na tara da suka fafata a ranar Lahadi a Goodison Park.

Rooney ne ya fara ci wa Everton kwallo a minti na 12 kuma na 12 jumulla da ya ci Arsenal har da wadanda ya ci a Manchester United.

Arsenal ta farke ta hannun Nacho Monreal kafin a tafi hutu, kuma bayan da aka dawo ne Ozil da Lacazette da Ramsey da kuma Sanchez suka ci daidai kowannensu.

Sai dai kafin Sanchez ya ci kwallonsa, Everton ta zare daya ta hannun Oumar Niasse bayan da Monreal ya mayar da tamaula gida, amma ba ta kai ga mai tsaron raga Arsenal da wuri ba.

Da wannan sakamakon Arsenal ta koma ta biyar a kan teburi da maki 16, bayan da ta yi nasarar cin wasa biyar ta yi canjaras daya aka doke ta sau uku.

Haka kuma Arsenal ta ci kwallo 17 a kakar bana an kuma zura mata 12, bayan kammala wasa tara a gasar.

Labarai masu alaka