Tottenham ta lallasa Liverpool

Harry Kane Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Harry Kane ne dan wasan da ya fi kowa cin kwallaye a kakar Premier bana, inda yake da kwallaye takwas

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta lallasa Liverpool da ci 4-1 a filin wasa na Wembley a gasar Premier.

Harry Kane ya fara zura wa Liverpool kwallo a raga minti hudu da fara wasan, daga nan ne Hugo Lloris ya ci wa Tottenham kwallo ta biyu a minti na 12.

A minti na 24 Salah ya farke wa Liverpool kwallo guda, wasan ya koma 3-1 ne yayin da Dele Alli ya ci tasa kwallon ana gab da zuwa hutun rafin loakci.

Bayan da aka dawo ne Kane ya kara cin kwallonsa ta biyu a wasan a minti na 56, inda wasa ya koma 4-1.

Sakamaon wasanya ya sa Tottenham ta koma maki 20 daidai da Manchester United wadda take mataki na biyu.

Labarai masu alaka