Mata 100: Me ya sa ba a biyan 'yan wasa mata sosai kamar maza?

Serena Williams and Cristiano Ronaldo holding trophies Hakkin mallakar hoto Getty Images

A jerin masu wasan motsa jiki da aka fi biya, mace daya ce take cikinsu - wato shahararriyar 'yar kwallan tennis Serena Williams.

Serena tana mataki na 51 kuma kudin da take samu ya gaza na Cristiano Ronaldo, dan wasan da ya fi samun kudi a duniya a cewar mujallar Forbes.

Tawagar mata 'yan kwallon kafa ta kasar Amurka ta samu kyautar dala miliyan biyu bayan ta ci gasar kwallon kafa ta duniya a shekarar 2015.

Har ila yau, gasar kwallon kafa ta duniya ta maza kuma ta samar wa wadanda suka lashe kyautar dala miliyan 35 a shekarar 2014.

Wadannan 'yan misalai ne kawai da ke nuna gagarumin gibin biya a duniyar wasanni da ya dade da zama al'ada.

Sai dai kuma, bincike na baya-bayan nan, ya nuna cewa bambanci wajen samun kudin shiga tsakanin 'yan wasa mata da 'yan wasa maza ya ragu sosai a 'yan shekaraun da suka wuce.

Hakkin mallakar hoto Harry How/GETTY IMAGES
Image caption Kwallon kafar mata ta fi farinjini a Amurka a kan ta maza - duk da haka tawagar kwallon mata ta kasar ba ta samun kudin da ya kai ta tawagar maza

Jumullar kashi 83 cikin 100 na wasanni a duniya yanzu suna biyan maza da mata kudi bai daya, in ji wani bincike kan fannoni 68 da sashen wasanni na BBC ya wallafa a watan Yunin da ya gabata.

Kudin da ake biyan mata yana karuwa ne tun shekara uku da suka wuce, kuma 35 daga cikin wasanni 44 da suka bayar da kyautar kudi suna biya bai daya ne.

Wannan ya yi kama da labari mai kyau, musammann idan aka kwatanata da shekarun da suka gabata - a shekarar 2014 kashi 70 cikin 100 na wasanni ne kawai suka samu suka cike gibin kudin biya,

Kuma a shekarar 1973 babu wani wasan da ya biya maza da mata bai daya.

"Mata sun fi fitowa a wasanni yanzu fiye da ko wane lokaci a tarihi," in ji wata sanar daga Hukumar Kula da mata ta Majalisar Dinkin Duniya.

Duk da haka sauyi na tafiyar hawainiya ta yadda za a dauki dogon lokaci kafin a kai ga samun biya bai daya a mataki na sama, in ji masana.

"Muna samun ci gaba, amman yana faruwa ne kamar tafiyar hawainiya," in ji Fiona Hathorn, darakatar kungiyar Women on Boards da ke fafatukar ganin mata suna shugabanci.

"Har yanzu duniyar wasanni ta kasance cike da maza a kan mata, kuma bambanci tsakanin maza da mata a wasu wasanni na da tayar da hankali sosai."

Hakkin mallakar hoto Shaun Botterill/ GETTY IMAGES
Image caption An bar mata masu buga kwallon Kriket baya idan ana maganar biya bai daya

Kriket da Golf da kuma kwallon kafa suna cikin wadanda suka fi sabawa biya bai daya tare da snuka da sauransu.

Kasuwancin wasanni na duniya - da ya kai dala biliyan 145.3 , in ji kiyasin PwC- bai kai ga samar da daidaito tsakanin jinsin maza da mata ba.

"Ba zan iya tunanin wani fannin da yake da irin wannan gibin ba. Ya danganci irin halin da ake ciki a kasa da kuma wasa, na miji ka iya zaman biloniya kuma mace (wadda take irin wasan) ba za ta iya samun albashi mafi karanci ba," in ji Beatrice Frey, manajar hadin gwiwa na wasanni a hukumar da ke kula da mata ta Majalisa Dinkin Duniya.

Wadanda suka fi laifi

Bambance-bambance suna fitowa karara a wane mataki na harkar kwallon kafa mai biloyoyin kudade.

Hakkin mallakar hoto David Ramos/GETTY IMAGES
Image caption Real Madrid ta samu kyautar dala miliyan 18 domin ta ci kofin gasar zakaarun Turai a kakar bara, yayin da wadanda suka lashe gasar ta mata, Lyon, suka samu kasa da dala 300,000

Wani bincike na kwanan nan da kungiyar Women on Boards ta fitar ya nuna cewa maza masu taka leda sukan samun abin da ya rubanya na mata sau hudu duk da cewa matan sun fi su kokari.

Gibin zai kara girma idan aka yi la'akari da jumullar kudin da aka biya.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ce take yanke iya kyautar da za a bayar a dukkan gasa biyun.

Ita ce ta ba da dala miliyan 15 ga wadanda suka lashe gasar kwallon kafa ta duniya ta mata, kuma ta ba da dala miliyana 576 ga wadanda suka lashe gasar kwallon kafa ta maza.

Kuma a daidai lokacin da kyaftin din Ingila, Wayne Rooney, yake samun kudi dala 400,000 a ko wane mako, albashin takwararsa mace, Steph Houghton, bai taka kara ya karya ba idan aka yi la'akari da nashi - kimanin dala 1,600 a ko wane mako, in ji kafar Ladbrokes Sports.

Ana iya ganin irin wadannan gibin biya a wasu wasannin.

A wasan Golf, maza a gasar US Open suna neman samun kyuatar kusan dala miliyan $1.5 ne, kudin da ya rubanya kyautar da mata za su samu a gasar.

Ka dubi labarin Lydia Ko, daga kasar New Zealand, wadda ta zama mai karamar shekaru irin nata cikin ko wane jinsi da ta fara zama cikakkiyar 'yar wasan Golf a shekarar 2015.

A wanna shekarar ta samu kudin da ya gaza na dan wasan golf da ke matsayi na 25 a jerin sunayen gwanaye cikin maza na gasar PGA Tour, kamar yadda Newsweek ta bayyana.

Har ila yau, a gasar Kriket wata tawagar maza da ta lashe gasar cin kofin duniya za ta iya rubanya abin da mata za su samu fiye da sau bakwai.

Kuma ana maimaita gibin albashin a gasar kwallon kwando ta maza da ta mata da ta fi daraja duniya - NBA da WNBA.

"'Yar wasan da ta fi samun kudi a gasar kwallon kwando ta WNBA tana samun kashi daya cikin biyar na abin da dan wasan kwallon kwandon da yake karbar kudi mafi karanci a gasar maza NBA," in ji mujallar NBA .

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption LeBron James ne dan wasa na biyu da ya fi arziki a tsakanin 'yan wasan motsa jiki na duniya in ji Forbes

'Kulob din yara'

Domin a samu daidaito, masana sun ce, bayar da kyaututtuka ba tare da la'akari da jinsi ba bai zai isa ba wajen kawar da matsalar sai an hada da daukar nauyi da talla da kuma sharuddan yarjejeniya.

Alal misali a fagen tennis, muhimman gasar da ake yi a ko wace shekara sun kaddamar da biya bai daya ga mata da maza tun shekarar 2007, duk da haka fitattun 'yan wasa maza sun fi mata samun kudi a ko wace shekara domin yarjejeniyoyi na daukar nauyi domin talla.

Shi ya sa Serena Williams ta kasance ita kadai a jerin sunayen 'yan wasa 100 da suka fi kudi ta mujallar Forbes.

"'Jerin 'yan wasa 100 da ke kan gaba ya fi zama na maza fiye da yadda aka saba", in ji wakilin mujallar Forbes kan wasanni Kurt Badenhausen a lokacin da aka fitar jerin sunayena watan Yuni.

"Maria Sharapova ta kasa shiga cikin jerin sunayen bayan an rage kudaden yarjejeniyoyin tallan da take da su."

Hakkin mallakar hoto Lintao Zhang/GETTY IMAGES
Image caption An soke kwantiragin tallan 'yar Rasha Maria Sharapova bayan an dakatar da ita na tsawon wata 15 sakamakon faduwar da ta yi a gwajin kwaya

Ronaldo ya samu dala miliyan 58 na alabashi da kyaututa, amman ya kara da dala miliyan 35m daga masu talla da masu daukar nauyi domin talla da kuma kudaden fitowa.

Ga kuma dan wasan golf Tigers Woods da kuma tauraron wasan tsere Usain Bolt, daukar nauyi domin talla ya kai kashi 90 cikin 100 na kudaden shigansu.

"Nuna wariyar jinsi ya zama ruwan dare gama duniya a fagen wasanni," in ji Frey.

"A matakin farko zai iya kasancewa domin mata ba sa iya wasannin da a al'adance ba na mata ba ne, lamarin da yake janyo wariya a tun suna kanana wanda zai bi su har zuwa lokacin da suka zama matasa zuwa gwanayen wasa."

Sannan, ta ce, yana nufin za a samu rashin daidaito a damarmaki a daukar nauyi da talla, har ya kai ga yawancin 'yan wasa mata a fadin duniya ba sa iya ciyar da kansu daga sana'o'insu na wasanni.

Hakkin mallakar hoto Thos Robinson/GETTY IMAGES
Image caption Taurariyar kwallon kafa ta Amurka mai murabus Abby Wambach ta buga wani littafin tarihinta kuma tana samun gayyata na halartan tarurruka - amman mata 'yan wasa da yawa ba sa samun irin wadannan damarmakin bayan sun yi murabus

Kuma yanayin na ta ci gaba.

"Ga mata 'yan wasa da suka yi murabus lamarin na tare da matsaloli. Bawai ba su samu kudi mai yawa ba ne kawai,ta yiwu ba su fansho ko gida ko kuma tsaro ba," in ji Hathorn.

"Kuma wannan wata matsala ce ga burin 'yan mata: me ya sa za su so zama 'yan wasa in har haka makomarsu za ta kasance?"

Yadda za a gane gibin

Za a iya ga ni tushen wannan gibin shi ne daga asalin wasannin zamani da kansu.

Al'ummomi daban-daban suna ganin atisaye a matsayin wani aiki da ke da alaka da namiji mai karfi, wanda yake da bambanci da mace mai rauni.

Hakkin mallakar hoto Hulton Archive
Image caption 'Yar Birtaniya, Charlotte Cooper Sterry, ta zama mace ta farko da fara zama zakarar wasan Olympics a shekarar 1900

Wanda za a iya cewa baban gasar Olympics na zamani, Pierre de Coubertin, ya bayyana wasannin mata a matsayin wani abin da ba shi da dadin gani kuma yana ganin shigan mata zai sa gasar ta rasa armashinta duk da cewa an bawasu mata kadan su shiga gasar Olympics a shekarar 1900.

A wancen lokacin mata suna shiga gasar tseren mita 1,500 domin ana ganin ba su shirya wa tseren da ya fi haka tsawo ba.

Ta fannin wakilci, sai gasar Olympics da aka gudanar a birnin Landan a shekarar 2012 ne ko wace kasa ta saka akalla mace daya a cikin 'yan wasanta na zuwa gasar.

Saboda haka za a iya alakanta gibin biya ga rashin daidaito na cikin jama'a - wanda ya fa rawar da mata suke takawa a wasanni yake kasa da na maza a kullum.

"Takarawar wata matsala ce wadda take farawa tun a shekarun da matan suke makaranta: a wanna lokacin ne yake farawa," in ji Ruth Holdaway, shugabar kungiyar Women in Sport da ke fafutukar kare 'yancin mata a wasanni.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kusan rabin matan sukan barin wasanni a lokacin da suka balaga, in ji wani bincike a Birtaniya

Lamarin na da alaka ne da yadda suke ganin jikinsu da yadda ake ganinsu da kuma irinwariyar da suke fuskanta, in ji Holdaway.

Alkaluma daha hukumar kula da mata ta Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa kashi 49 cikin 100 na 'yan mata suna barin wasanni a lokacin da suka balaga, kuma wannan yana da tasiri a kan yawan wadanda za su zama kwararrun 'yan wasa daga cikinsu a gaba

Kunna talabijin

An yarda cewa yawan gibin biya na jinsi yana da nasaba da kasuwancin da ake yi da wasannin, inda sayan 'yancin watsa wasa yake taka muhimmiyar rawa.

Wani binciken da jami'ar cibiyar bincike kan 'yan mata da matan da ke wasanni ta Tucker Centre da ke jami'ar Minnesota ta gano cewa a shekara 2014 kashi hudu daga cikin 100 ne gurbin da wasannin mata suka samu a kafafan watsa labarai duk da cewa kashi 40 cikin 100 na masu wasan mata ne.

Hakkin mallakar hoto Doug Pensinger/GETTY IMAGES
Image caption Yawancin muhimman 'yancin wasa na taimakawa wajen biyan 'yan wasa

Kuma cikin dan lokacin da suka samu akwai yiwuwar cewa za a nuna wariyar jinsi a wajen watsa wasannin mata, ta hanyar nuna 'yan wasa a wajen fili da kuma cikin kayan gida inda ake mayar da hankali kan yadda suke da kyau a jiki maimakon iya wasansu", in ji daraktan Tucker Centre, Mary Jo Kane.

Sabaoda haka, mutane da yawa za su ce matana ba sa samun kudi kaman maza saboda haka kasuwar take so saboda wasanni mata ba su da farin jini irin na maza, kuma ssaboda haka wasannin suna samun kudin shiga wanada bai kai na maza ba.

Mene ne shirin Mata 100?

Shirin Mata 100 yana bayyana sunayen mata 100 wadanda suka yi zarra da tasiri a fadin duniya kowace shekara.

A shekarar 2017, muna bukatarsu da su magance wadansu manyan batuwa guda hudu da suke jawo wa mata cikas a yanzu - cimma wani babban mataki da batun ilimi da batun cin zarafi da kuma nuna wariya musamman a fannin wasanni.

Da taimakonmu, za su lalubo hanyoyin magance matsalolin kuma muna so su ba da gudunmuwa da shawarwari.

Za a iya tuntubar mu a shafukanmu na Facebook da Instagram da Twitter da kuma ta hanyar amfani da maudu'in #100Mata


Wadansu daga cikin mutanen da ke cikin jerin Mata 100 za su yi aiki ne daga birane hudu a tsawon mako hudu na watan Oktoban bana, inda za su samar da hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalolin.

Sauran za su ba da gudunmuwarsu daga sauran sassan duniya.

Za a bayyana ragowar sunayen mata 40, yayin da mata ke ci gaba da shiga shirin da kuma ba da gudunmuwarsu da kwarewarsu.