Everton ta kori kocinta Koeman

Everton Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Everton ta bai wa Ronald Koeman aikin jan ragamarta tun kafin fara gasar 2016/16

Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta sallami kocinta Ronald Koeman, bayan da ya yi rashin nasara da ci 5-2 a hannun Arsenal a ranar Lahadi a gasar Premier.

Doke Everton da Arsenal ta yi ya sa kungiyar ta koma kasan teburi ta 18, bayan da ta ci wasa biyu a karawa tara da ta yi a gasar ta Premier.

Koeman mai shekara 54 ya ja ragamar Everton ta kare a matsayi na bakwai a gasar Premier ta bara, kuma a bana ya kashe fam miliyan 140 wajen sayo sabbin 'yan kwallo.

Koeman ya zama koci na uku da aka sallama daga aiki a gasar Premier a bana, bayan Frank de Boer da Crystal Palace ta kora da Craig Shakespeare wanda ya raba gari da Leicester City.

Labarai masu alaka