Super Eagles za ta kara da Argentina

Super Eagles Hakkin mallakar hoto The NFF
Image caption Super Eagles za ta buga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2017

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria za ta buga wasan sada zumunta da ta Argentina a birnin Krasnodor na Rasha a ranar Talata.

Super Eagles za ta buga karawar ce, bayan da ta tashi 1-1 da Algeria a wasan shiga gasar cin kofin duniya, wacce tuni Nigeria ta zama ta farko da ta samu tikitin kai wa Rasha.

Wannan wasan sada zumunta zai zama na fara shirin gasar kofin duniya ne da Nigeria ta ta wakilci Afirka a badin.

Sakatare janar na hukumar kwallon kafar Nigeria, Dakta Muhammadu Sunusi ya ce kasashe kamar su Iran da Saudi Arabia da Morocco duk sun nemi su buga wasan sada zumunta da Nigeria, amma ta zabi ta fuskanci Argentina.

Nigeria da Argentina sun kara a wasan sada zumunta a 2011, inda wasan farko a Abuja Super Eagles ta ci 4-1 a watan Yuni, karawa ta biyu kuwa Argentina ce ta yi nasara da ci 3-1 a Bangladesh a watan Satumba.