Tottenham za ta tsugawa Kane kudi — Perez

Tottenham
Image caption Madrid da Tottenham sun buga 1-1 a gasar cin kofin Zakarun Turai da suka kara a Spaniya

Shugaban kungiyar Real Madrid, Florentino Perez ya ce Tottenham za ta saka kudi mai tsada ga duk kungiyar da ke son sayen Harry Kane.

Da aka tambayi Perez ko ya tattauna da shugaban Tottenham, Daniel Levy kan nawa za a sayar masa da dan wasan sai ya ce bai yi ba, amma za a ce ya biya fam miliyan 223.

Sai dai kuma shugaban na Real Madrid ya ce bai taba tunanin kawo Kane Santiago Bernebeau domin ya taka-leda ba.

Kocin Madrid, Zinedine Zidane ya ce Kane cikakken dan kwallo ne tun kafin su fafata a gasar cin kofin Zakarun Turai da suka tashi 1-1 a Spaniya.

Kane ya ci wa Tottenham da tawagar Ingila kwallo 15 tun fara kakar bana, ya kuma ci 45 jumulla a shekarar 2017.

A bana ne Paris St Germain ta sayi Neymar daga Barcelona kan kudi fam miliyan 200 a matsayin wanda aka saya mafi tsada a duniya

Labarai masu alaka