Phil Neville na son karbar aikin kocin Everton

Phil Neville Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Phil Neville ya taka-leda sau 303 a Everton bayan da ya koma can daga Manchester United a 2005

BBC ta fahimci cewa tsohon dan wasan Everton Phil Neville na son karbar aikin kocin kulob din.

Kulob din Everton ya kori Ronald Koeman ranar Litinin bayan da Arsenal ta doke su a gasar Firimiya.

Rashin nasarar ya jefa kungiyar sahun kulob uku da ka iya faduwa a gasar idan suka kare a haka.

Tsohon dan wasan na Ingila Naville, mai shekara 40, ya taka-leda fiye da sau 250 a Everton a shekara takwas da ya shafe a kulob din.

A baya ya taba zamowa mataimakin koci a kungiyar Valencia ta La Ligar kasar Spaniya.

A ranar Talata ne Everton ta tabbatar da cewa kocin tawagar 'yan kasa da shekara 23 David Unsworth zai ci gaba da jan ragamar kulob din a matsayin riko.

Zai kuma fara jan ragamar kulob din a wasan da za su yi ranar Laraba a gasar cin kofin Carabou da Chelsea.

Rahotanni sun nuna cewa Ryan Giggs ma ya nuna sha'awarsa kan aikin, hakazalika ana kuma alakanta kocin Burnley Sean Dyche da tsohon manajan Bayern Munich Carlo Ancelotti da aikin na Everton.

Labarai masu alaka

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba