World Cup U-17: Brazil ta yi ta uku bayan da ta ci Mali

World Cup u17 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Brazil ce ta uku sai Mali ta hudu a gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan 17 a India

Tawagar kwallon kafa ta Brazil ta yi nasarar doke ta Mali 2-0 ta kuma zama ta uku a gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan 17 da suka kara a India.

Brazil wacce ta yi rashin nasara a hannun Ingila a wasan daf da karshe ta ci Mali ne ta hannun Alan fortuitous da kuma Yuri Alberto a fafatawar da suka yi a Kolkata a ranar Asabar.

Mali wacce ta yi rashin nasara a wasan daf da karshe a hannun Spaniya ta zama ta hudu a gasar ta matasa ta duniya, duk da cewar ita ce zakara a nahiyar Afirka.

Za a buga wasan karshe tsakanin Ingila da Spaniya.

Labarai masu alaka