Arsenal tana ta biyar a kan teburin Premier

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ramsey ya ci kwallo a karawar da Arsenal ta doke Everton 5-2

Arsenal tana a mataki na biyar a kan teburin Premier, bayan da ta doke Swansea City da ci 2-1 a wasan mako na 10 da suka kara a ranar Asabar a Emirates.

Swansea ce ta fara cin kwallo ta hannun Sam Clucas, bayan da aka dawo ne Arsenal ta farke ta hannun Sead Kolasinac daga baya Aaron Ramsey ya kara ta biyu.

Wasan wanda shi ne na 800 da Arsene Wenger ya ja ragamar Arsenal ya sa ta samu maki uku a ranar Asabar, sannan 19 jumulla a wasa 10 da ta buga ta kuma koma ta hudu a teburi.

Chelsea ce ta hudu bayan da ta ci Bournemouth daya mai ban hausi a karawar mako na 10.

Labarai masu alaka