'Yan Madrid da za su kara da Tottenham

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid da Tottenham suna da maki bakwai-bakwai a rukuni na takwas

Tun a sanyin safiyar Talata Real Madrid ta sauka a Ingila domin shirin karawa da Tottenham a wasa na biyu na cikin rukuni a gasar cin kofin Zakarun Turai da za suyi a ranar Laraba.

Wasan farko da suka kara a Bernabeu kungiyoyin biyu sun tashi ne kunnen doki daya da daya.

Kuma Real Madrid da Tottenham suna kan teburin rukuni na takwas da maki bakwai-bakwai kuma duk wacce ta yi nasara za ta kai wasan zagaye na biyu.

Tuni kocin Madrid, Zinedine Zidane ya isa Ingila da 'yan wasa 19 da yake sa ran fuskantar Tootenham da su.

Ga jerin 'yan wasan da Real Madrid

Masu tsaron raga: Casilla da kuma Moha.

Masu tsaron baya: Vallejo, Sergio Ramos, Nacho, Marcelo, Theo da kuma Achraf.

Masu wasan tsakiya: Kroos, Modric, Casemiro, M. Llorente, Asensio, Isco da kuma Ceballos.

Masu cin kwallo: Cristiano Ronaldo, Benzema, Lucas Vázquez da kuma Mayoral.