Super Eagles ta gayyaci Ahmed Musa da 'yan wasa 23

World Cup Russia

Asalin hoton, The NFF

Bayanan hoto,

Nigeria ce ta farko da ta fara samun tikitin zuwa Rasha domin buga gasar kofin duniya a 2018

Kocin tawagar kwallon kafar Nigeria, Gernot Rohr ya gayyaci 'yan wasa 24 domin karawa da Algeria a wasan shiga gasar cin kofin duniya da wasan sada zumunta da Argentina.

Super Eagles wacce tuni ta fara samun tikitin shiga gasar kofin duniya daga Afirka, za ta buga wasan karshe na cikin rukuni da Algeria a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Haka kuma kwana hudu tsakani wato ranar 14 ga watan Nuwamba, Nigeria za ta buga wasan sada zumunta da Argentina wanda za su kece raini a birnin Krasnodar na Rasha.

Super Eagles ta gayyaci sabbin 'yan wasa da suka hada da Francis Uzoha da ke wasa a Deportivo La Coruna da tsohon dan wasan matasa 'yan 17, Chidiebere Nwakali.

Shi kuwa Brian Idowu zai yi jiran ko ta kwana a wasan sada zumunta da Argentina.

An bukaci dukkan 'yan wasan da aka gayyata da su iya sansanin horo a Morocco a ranar 6 ga watan Nuwamba, daga nan su iya Algeria a ranar 9 ga watan na Nuwamba.

Ga jerin 'yan wasan da Super Eagles ta gayyata:

Masu tsaron raga: Daniel Akpeyi (Chippa United, South Africa); Ikechukwu Ezenwa (FC IfeanyiUbah); Francis Uzoho (Deportivo La Coruna, Spain)

Masu tsaron baya: William Ekong (Bursaspor FC, Turkey); Abdullahi Shehu (Anorthosis Famagusta, Cyprus); Tyronne Ebuehi (ADO Den Haag, The Netherlands); Leon Balogun (FSV Mainz 05, Germany); Uche Agbo (Standard Liege, Belgium); Chidozie Awaziem (Nantes FC, France); Olaoluwa Aina (Hull City, England)

Masu wasan tsakiya: Mikel John Obi (Tianjin Teda, China); Ogenyi Onazi (Trabzonspor FC, Turkey); Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Oghenekaro Etebo (CD Feirense, Portugal); John Ogu (Hapoel Be'er Sheva, Israel); Mikel Agu (Bursaspor FC, Turkey); Chidiebere Nwakali (Sogndal FC, Norway)

Masu cin kwallo: Ahmed Musa (Leicester City, England); Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Moses Simon (KAA Gent, Belgium); Alex Iwobi (Arsenal FC, England); Odion Ighalo (Chang Chun-Yatai, China); Henry Onyekuru (RSC Anderlecht, Belgium); Anthony Nwakaeme (Hapoel Be'er Sheva, Israel)

Masu jiran ko ta kwana: Kenneth Omeruo (Kasimpasa FC, Turkey); Alhassan Ibrahim (FK Austria Wien, Austria); Brian Idowu (FC Amkar Perm, Russia)