Man Utd v Benfica: 'Yan United ba sa rububin fanareti - Morinho

Daley Blind scores a penalty for Manchester United

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Lukaku wanda United ta saya a kan kudi fam miliyan 90, na fatarar cin kwallo a raga

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce babu wata matsala akan matakinsa na haramtawa Rumelu Lukaku buga fanariti bayan dan wasan ya buga wasanni shida ba tare da ya ci wa kungiyar kwallo a raga ba.

Lukaku wanda United ta saya a kan kudi fam miliyan 90, na fatarar cin kwallo a raga.

Sama da tsawon wata daya rabon da Lukaku ya ci wa United kwallo a raga, matakin da ya sa ya fara fuskantar suka daga magoya bayan kungiyar.

Rabon Lukaku da ya jefa kwallo a raga a United tun a watan Satumba.

Kalubalen da Lukaku ke fuskanta ya fara tsananta inda Daley Blind ya ci wa United Fanariti a wasan da suka doke Benfica ci 2-0 duk da Lukaku ne ya fara shirin buga fanaritin.

Mourinho ya yanke shawarar cewa Blind ne zai ci gaba da buga Fanariti a wasannin Manchester United.

Kuma a cewar kocin, matakin da ya dauka shi ne karshe.

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Sama da tsawon wata daya rabon da Lukaku ya ci wa United kwallo a raga

Mourinho ya ce matakinsa ba zai haifar da rabuwar kai ba tsakanin 'yan wasansa.

Wannan dai na zuwa kwana guda bayan Mourinho ya yi jinjina ga Lukaku wanda ya ci kwallaye 11 a wasanni 10 da ya buga wa Manchester a kakar bana.