Chelsea ba ta da kishirwar cin kwallo — Conte

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Chelsea tana ta biyu a rukuni na uku da maki bakwai a gasar cin kofin Zakarun Turai

Antonio Conte ya ce ya kamata Chelsea ta dawo da kishirwar cin kwallaye, bayan da Roma ta doke ta da ci 3-0 a gasar cin kofin Zakarun Turai a ranar Talata.

Cikin kwallo ukun da Roma ta ci Chelsea, Stephan El Shaarawy ne ya ci biyu, kuma hakan ya sa kungiyar ta Stamford Bridge ta koma ta biyu a kan teburin rukuni na uku.

Chelsea za ta kai wasan zagaye na biyu idan har ta doke Qarabag a wasan gaba da za ta buga a gasar ta Zakarun Turai.

Conte ya ce duk wata babbar kungiya ya kamata ta samu natsuwa da juriya da hadin kai, a koda yaushe.

Kocin dan Italiya ya lashe kofin Premier na bara a kakar farko da ya ja ragamar kungiyar, kuma wasa biyar aka doke shi cikin 38 da ya buga.

Chelsea wacce ta yi rashin nasara a wasa uku daga 10 da ta yi a Premier bana, za ta karbi bakuncin Manchester United a ranar Lahadi.