Wai me ke faruwa da Real Madrid ne?

  • Awwal Ahmad Janyau
  • BBC Abuja
'Yan wasan Tottenham

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dele Alli, na uku daga hagu, ya zura kwallo biyu a wasan da Tottenham ta ci 3-1 a Wembley

Halin da Real Madrid ta samu kanta a kakar bana na cigaba da jan hankalin masu sha'awar kwallo bayan da kungiyar ta sha kashi a wasa biyu a jere a gasar Zakarun Turai da La liga.

Tottenham ta casa Madrid da ci 3-1 a wasannin rukuninsu na H, kuma wannan na zuwa ne bayan da zakarun na Turai da La liga suka sha kashi a karshen mako a hannun Girona a gasar Lig.

Wannan shi ne karo na farko da wata kungiya ta ci Madrid a wasannin rukuni a gasar Zakarun Turai tun kashin da ta sha a hannun Borussia Dortmund a shekarar 2012.

An shafe tsawon shekara tara kuma, rabon da wata kungiya ta zazzagawa Madrid kwallaye a raga a wasannin rukunin gasar Zakarun Turai tun lokacin da Juventus ta ci ta 2-0 a 2008.

Karon farko ke nan da aka doke Madrid a wasanni biyu jere tun a watan Janairu da ta sha kashi a hannun Sevilla a La Liga da kuma Celta Vigo a Copa del Ray.

Masharhanta dai na ganin canjin salo ne aka samu sabanin rawar da kungiyar ta taka karkashin Zidane a shekara biyu da ta gabata inda ya lashe kofuna biyu na Zakarun Turai da kuma kofin La liga.

Halin da Madrid ke ciki a yanzu na iya kasancewa babban kalubalen da Zinaden Zidane ke fuskanta, duk da ya ta taka rawar gani a kaka biyu da suka gabata.

Wasu magoya bayan kungiyar na ganin matsalolin da kungiyar ke fuskanta a yanzu, na da nasaba da sakin wasu manyan 'yan wasa da Zidane ya yi kamar Alvaro Morata da Danilo da James Rodriguez da Pepe.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid ta shafe wasa 30 rabon da a doke ta a wasannin rukuni a gasar Zakarun Turai

Alhaji Danjuma Muhammad wani mai goyon bayan kulob din ya ce ba ya jin dadin yadda abubuwa ke tafiya domin an sayar da 'yan wasa ba tare da kawo madadinsu ba.

"Wasa yana mana hawala, a zo gida a ci mu kuma haka ma a waje", kamar yadda ya shaida wa BBC.

Baya ga wannan kuma, wasu na ganin akwai manyan 'yan wasan kungiyar da suka dan fara gajiya irinsu Tony Kroos, da raunin da Gareth Bale da Benzema suke yawan samu.

Ana ganin Tottenham ta samu galaba akan Madrid saboda rashin isassun kwararrun 'yan wasa a bencin Madrid, al'amarin da Danjuma ke ganin ya dace kungiyar ta gyara a watan Janairu idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallo.

Magoya bayan kulob din a sassan duniya daban daban na ci gaba da nuna damuwarsu kan halin da ya shiga.

Sai dai wasu na cewa wannan ba wani abin damuwa ba ne, kuma za su dawo kan ganiyarsu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kocin Real Madrid Zinadine Zidane ka iya shiga tsaka mai wuya idan bai gyara lamura da wuri ba

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Dele Alli ya zura kwallo ta shiga a Tottenham a kakar bana

Yanzu maki takwas ne Barcelona ta ba Real Madrid a teburin La Liga, kuma a Disamba ne kungiyoyin biyu za su hadu a wasan hamayya na Clasico.

Wasanni biyu suka rage a kammala karawar rukuni a gasar zakarun Turai, kuma Zidane ya amsa cewa kungiyarsa na cikin hali na damuwa.

Sai dai kuma kocin ya ce ba wani abin shan kai ba ne domin kowa ya san matsayin Madrid a fagen tamola.

Wasu sharhi na ganin idan har kocin bai yi wani hobbasa wurin gyara al'amura ba, to mai yi wuwa makomarsa ta shiga cikin rudani duk da nasarorin da ya samu a baya.