An kawo karshe shari'ar da ake min - Mourinho

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jose Mourinho ya je kotun ne kwana biyu kafin wasan United da Chelsea

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce an kawo karshen shari'ar da ake yi masa kan zargin aikata zamba wurin biyan haraji a kasar Spaniya a lokacin da ya ke Real Madrid.

Ya fito bayan wani gajeren zaman jin bahasi a wata kotu da ke birnin Madrid inda ya ce ya biya wasu kudade domin kawo karshen zarge-zargen.

An dai yi zargin cewa ana bin sa kimanin dala miliyan 3.8 kan wasu kudaden shiga da ya samu a kan hakkokin mallakar wasu hotunansa da bai bayyana ba.

Sai dai da farko wakilansa sun yi watsi da zargin da babbar murya.

Zaman kotun na zuwa ne kwana biyu kafin wasan Manchester United da Chelsea a gasar Firimiya.

Kocin ya sauya ayyukan da yake yi gabannin wasan da kungiyarsa za ta buga, inda ya gabatar da taron manema labaransa a ranar Alhamis maimakon Juma'a kamar yadda aka saba.

Rahotanni sun ce an shaida wa 'yan wasan Manchester United cewa an sauya lokacin atisayensu.

Jami'an kasar Spaniya sun fara binciken Mourinho ne a watan Yuni.