Masu sukar mu ba sa yi mana adalci — Mourinho

Man United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

United tana ta biyu a kan teburin Premier, tana ta daya a teburin farko a gasar Zakarun Turai

Kocin Manchester United, Jose Mourinho, ya ce ana amfani da ma'auni na daban wajen auna kwazon kungiyarsa idan aka kwatanta da wasu kungiyoyin.

Mourinho na shan suka game da salon taka-leda na United, musamman a wasan da ta yi canjaras da Liverpool da yadda ta ci Benfica da kyar da doke Tottenham daya mai ban haushi.

A kalaman da ya rubuta game da zagaye na biyu na karawarsu da Benfica a gasar cin Kofin Zakarun Turai a Old Trafford Mourinho ya fada wa magoya bayan kungiyar cewa, ''Ina fatan za ku ji dadin wannan wasan fiye da yadda wasunku suka ji a karawarmu da Tottenham''.

Yayin wani taron manema labarai a kan wasan da za su buga da Chelsea a ranar Lahadi, ya sake tabo batun, ko da yake ya ce ba ya so ya kara jawo magana.

Wannan ne karo na hudu da Mourinho zai fuskanci tsohuwar kungiyarsa, Chelsea - da farko lokacin yana tare da Inter Milan, sai kuma sau biyu a bara yayin da yake tare da Manchester United.