Arsenal ta kai zagaye na biyu a gasar Europa

Europa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Arsenal ce ke jan ragamar rukuni na takwas a gasar ta Europa, ta kuma kai zagaye na biyu

Kungiyar Arsenal ta kai wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Europa duk da tashi wasa da ta yi babu ci tsakaninta da Red Star Belgrade a ranar Alhamis a Emirates.

A wasan farko da aka buga a Belgrade, Arsenal ce ta ci Red Star daya mai ban haushi, kuma Olivier Giroud ne ya ci kwallon.

Arsenal ta yi wasa 16 a dukkan karawa a Emirates ba tare da an doke ta ba, inda ta ci wasa 14 ta yi canjaras a fafatawa biyu.

Wannan ne karo na biyu da Arsenal ta kasa samun maki uku tun cikin watan Mayu da ta tashi 2-2 da Manchester City a gida.

Arsenal ce ta daya a rukuni na takwas da maki 10 a wasa hudu da ta buga, daya wasan cikin rukunin kuwa Cologne ce ta ci BATE Borisov 5-2.