Mourinho na fuskantar tuhumar kin biyan haraji

Mourinho

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mourinho ya zauna a Spaniya tsakanin shekarar 2010 da shekarar 2013

Ana tsammanin kocin Manchester United, Jose Mourinho, zai bayyana a gaban wata kotun Spaniya inda zai fuskanci tuhumar aikata ba daidai ba wajen biyan haraji a lokacin da yake kocin Real Madrid.

An yi zargin cewa ana bin sa kimanin fam miliyan 2.9 kan wasu kudaden shiga da ya samu a kan hakkokin mallakar wasu hotunansa da bai bayyana ba.

Sai dai wakilansa sun ki amincewa da zargin.

Har yanzu babu tabbacin cewa Mourinho zai halarci zaman kotun, amman ya sauya ayyukan da yake yi gabannin wasan da kungiyarsa za ta buga.

A wannan karon ya yi jawabin da ya saba yi wa manema labarai kafin wasa ne a ranar Alhamis maimakon ranar Juma'a.

Rahotanni sun ce an shaida wa 'yan wasan Manchester United cewa an sauya lokacin atisayensu.

Hukumomin Spaniya sun fara tuhumar Mourinho ne a watan Yuni, kuma an neme shi da ya bayyana a gaban wata kotun Madrid ne, kwana biyu kafin kungiyarsa ta Manchester United ta kai ziyara Chelsea a gasar Firimiya.