Buhari zai ziyarci yankin jihohin Igbo - Rochas Okorocha

Rochas Okorocha

Asalin hoton, Rochas Okorocha Twitter

Bayanan hoto,

Mista Okorocha ya ce Shugaba Buhari zai kai wannan ziyara ce domin ya inganta alakar mutanen yankin da jam'iyyar APC mai mulki

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari zai kai ziyara yankin 'yan kabilar Igbo da ke kudu maso gabashin kasar nan ba da jimawa ba.

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha wanda ya bayyanawa manema labarai hakan bayan sun fito daga wata ganawa da suka yi da shugaban a asirce a fadar gwamnati da ke Abuja.

Mista Okorocha ya ce Shugaba Buhari zai kai wannan ziyara ce domin ya inganta alakar mutanen yankin da jam'iyyar APC mai mulki.

A zantawar da ya yi da manema labarai bayan ya gana da shugaban kasar ranar Alhamis, gwamna Okorocha ya ce sun shirya dabarun da za su sa jam'iyyar APC ta samu karbuwa a yankin.

Ya bayyana bukatar da ke akwai ta ganin cewa Shugaba Buhari ya kai wannan ziyara a kurkusa.

Kazalika ya ce shugaban zai fara ziyarar tasa ne daga jihar Ebonyi daga bisani sai ya wuce jihohin Anambra da Imo.

"Mambobin jam'iyyar APC za su karu sosai a yankin kudu maso gabas, saboda yadda 'yan siyasa da dama ke ta komawa jam'iyyar a baya-bayan nan," in ji Mista Okorocha.

Gwamna Rochas ya kuma ce Shugaba Buhari ya cancanta wajen sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2019 a siyasance.

Yankin kudu maso gabashin Najeriya dai nan ne yankin da ake samun masu fafutukar kafa kasar Biafra karkashin jagorancin kungiyar IPOB ta Nnamdi Kanu.

Kuma tun bayan fara fafutukar tasu ake ta dauki ba dadi tsakanin 'yan kungiyar da sojojin Najeriya.

Tun bayan da Shugaba Buhari ya dare mulkin Najeriya shekara biyu da rabi dai ya yi tattaki ne kawai zuwa wasu jihohin 'yan kalilan a wasu sassan kasar.

Sai dai wannan ne karo na farko da ake sa ran zai kai ziyara zuwa yankin Kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo.

Amma 'yan kasar da dama sun dade suna sauraren ganin cewa Buhari ya kai ziyara yankin kudu maso gabas din da ma na kudu maso kudanci mai arziki man fetur, inda can ma ake fama da ayyukan masu tayar da kayar baya na Neja-Delta.