Za a yi gumurzu tsakanin Chelsea da Man United

  • Mohammed Abdu
  • BBC Hausa
Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Karo na uku kenan da Mourinho zai ziyarci Stamford Bridge tun bayan da Chelsea ta sallame shi

Kungiyar Chelsea za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan mako na 11 a gasar cin kofin Premier a ranar Lahadi a Stamford Bridge.

Manchester United tana ta biyu da maki 23 a kan teburin bana, bayan da ta ci wasa bakwai ta yi canjaras a karawa biyu aka doke ta sau daya.

Ita kuwa Chelsea tana ta hudu a kan teburi da maki 19, bayan da ta ci wasa shida da canjaras daya aka doke ta karo uku a wasannin shekarar nan.

Kungiyoyin sun kara sau uku a bara, inda United ta ci Chelsea 2-1 a Old Trafford a Premier, ita kuwa Chelsea ta doke United karo biyu, daya 4-0 a Premier da 1-0 a FA duk a Stamford Bridge.

Mourinho bai yi rashin nasara a fafatawa takwas da duk kungiyar da ke rike da kofin da ta ci bara ba, inda ya ci wasa uku da canjaras biyar.

Sai dai kuma sau daya Chelsea ta yi rashin nasara a wasa 15 a baya-bayan nan da ta buga da United, inda ta ci karawa tara ta yi canajaras biyar.