Man City da Arsenal za su kece raini ranar Lahadi

  • Mohammed Abdu
  • BBC Hausa
Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Man City tana ta daya a kan teburin Premier ita kuwa Arsenal tana ta biyar

Arsenal za ta ziyarci Ettihad a ranar Lahadi domin buga wasan Premier gasar mako na 11 da Manchester City.

Manchester City tana ta daya a kan teburi da 28 bayan wasa 10 da ta buga a gasar, hakan ya sa ta yi kan-kan-kan da tarihin hada maki irin haka a 2011, bayan da Chelsea ma ta yi hakan a 2005.

Arsenal kuwa tana mataki na biyar a kan teburin da maki 19, bayan da a bara a irin wannan yanayin Gunners ke matsayi na biyu da maki 23.

A bara da kungiyoyin suka fafata a gasar Premier sun tashi 2-2 a gidan Arsenal, sai City ta doke Gunners 2-1 a Ettihad, sannan Arsenal ta fitar da City daga gasar FA da ci 2-1.

Wannan ne karon farko da Pep Guardiola ya hada kwallo 35 a wasa goma da ya ja ragamar kungiya, tun bayan kwallo 34 da ya ci a Barcelona a kakar 2008/09.