Liverpool ta hada maki uku a kan West Ham

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rabon da Liverpool ta ci wasa biyu a jere tun watan Agusta bayan da ta doke Crystal Palace da Arsenal

West Ham United ta yi rashin nasara a gida a hannun Liverpool da ci 4-1 a gasar Premier wasan mako na 11 da suka kara a ranar Asabar.

Liverpool ta ci kwallayen ne ta hannun Mohamed Salah wanda ya ci biyu a wasan sai Joel Matip da Oxlade-Chamberlain kowannen su ya ci guda-guda

Ita kuwa West Ham ta zare kwallo daya ne ta hannun Manuel Lanzini bayan da aka koma wasa zagaye na biyu.

Da wannan sakamakon Liverpool ta hada maki 19 kenan bayan da ta ci wasa biyar da kunnen doki hudu da rashin nasara a karawa biyu.

West Ham tana nan da makinta tara karo na biyu da ta yi karancin maki bayan buga wasa 10 tun kakar 2011 lokacin da ta samu maki 10 a karawa 11 da ta buga, kuma a shekarar ta bar gasar Premier.

Liverpool za ta buga wasan mako na 12 a gida da Southampton a ranar Asabar 19 ga watan Nuwamba, a kuma ranar ce West Ham za ta ziyarci Watford.