Moyes na sha'awar horar da West Ham

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Moyes ya horar da Everton da Manchester United

David Moyes ya ce zai so ya zama kocin West Ham United, bayan da makomar Slaven Bilic ke cikin rashin tabbas.

Sashen wasanni na BBC ya fahimci cewar tuni kungiyar ta tattauna da Moyes tsohon kocin Everton da Manchester United.

Sai dai kuma a hira da ya yi da Bein Sports, Moyes ya musanta cewar ya tattauna da mahukuntan kungiyar, amma ya ce yana son ya zama kocin West Ham.

West Ham tana ta 17 a kan teburin Premier da maki tara, bayan da ta buga wasa 11, inda Liverpool ta doke ta 4-1 a gidanta a ranar Asabar.

Bayan kammala wasan koci Slaven Bilic ya ce yana cikin matsi kuma yana wani hali na tsaka mai wuya.