Shagon Shagon Lawwali ya buge Dan Sama'ila

Shagon Shagon Lawwali ya buge Dan Sama'ila

An dambata a wasanni da yawa a safiyar Lahadi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei Abuja, Nigeria.

Mohammed Abdu ne ya hada rahoton

Sai dai wasa uku ne suka fi jan hankalin 'yan kallo, inda Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa ya buge Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu a turmi na biyu.

Suna kammala dambe ne aka sa zare tsakanin Bahagon Aleka daga Kudu da Sani Mai Kifi daga Arewa, kuma Bahagon Aleka ne ya buge Sani Mai Kifi a turmin farko.

Wasa na uku da ya ja hankalin 'yan kallo shi ne tsakanin Dan Abata Mai karami daga Kudu da Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa, kuma turmi uku suka yi babu kisa aka raba su.