Arsenal ba ta sha da dadi ba hannu Man City

Man City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Aguero ya ci kwallo na 178 a wasa 264 da ya buga wa Manchester City

Manchester City ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier bana, bayan da ta doke Arsenal da ci 3-1 a wasan mako na 11 da suka kara a Ettihad a ranar Lahadi.

City ta fara cin kwallo ta hannun Kevin De Bruyne kafin a je hutu, bayan da aka dawo ne Sergio Aguero ya kara ta biyu a bugun fenariti, Arsenal ta farke daya ta hannun Alexandre Lacazette.

Manchester City ta ci kwallo ta uku ta hannun Gabriel Jesus, wanda hakan ya sa ta hada maki 31, ta kuma ci wasan Premier tara a jere.

City za ta ziyarci Leicester City a wasan mako na 12 a gasar ta Premier a ranar 18 ga watan Nuwamba.

Ita kuwa Arsenal wadda har yanzu tana ta biyar a kan teburi da maki19 za ta karbi bakuncin Tottenham a Emirates a ranar ta Asabar 18 ga watan Numbar 2017.

Labarai masu alaka