Conte ya doke Mourinho karo na uku a Ingila

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

United tana ta biyu a kan teburin Premier, ita kuwa Chelsea tana na hudunta a teburin

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi nasarar doke Manchester United 1-0 a gasar Premier wasan mako na 11 da suka kara a Stamford Bridge.

Chelsea ta ci kwallon ne ta hannun Morata, wanda hakan ya sa ta hada maki 22 a wasa 11 da ta buga a gasar, tana kuma nan a matakinta na hudu a kan teburi.

Manchester United tana nan a matsayinta na biyu da makinta 23, bayan da abokiyar hamayyarta Manchester City wacce ke mataki na daya ta ba ta tazarar maki takwas.

Wannan ne karo na uku da Antonio Conte ya yi nasara a kan Mourinho a Ingila, bayan da a bara Chelsea ta ci United 4-0 a Premier da kuma 1-0 a kofin FA.

Chelsea za ta ziyarci West Bromwich Albion a wasan mako 12 a ranar Asabar 18 ga watan Nuwamba, a kuma ranar ce United za ta karbi bakuncin Newcastle United.