West Ham ta sallami Bilic

West Ham

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An ci West Ham kwallo 23 a wasa 11 da ta buga a Premier tana kuma da maki tara

West Ham United ta kori Slaven Bilic daga aikin horar da kungiyar, bayan da ta fada cikin 'yan ukun karshen teburin Premier bana.

West ham ta sha kashi a hannun Liverpool a gida da ci 4-1 a gasar Premier wasan mako na 11 da suka fafata a ranar Asabar a London Stadium.

Kungiyar ta bayar da sanarwar cewar ya zama wajibi a kawo sauyi domin West Ham ta cika burinta a fagen tamaula.

Ana kuma alakanta David Moyes tsohon kocin Everton da Manchester United a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

West Ham tana ta 18 a kasan teburin Premier da maki tara kuma kwallo 23 aka zura a ragarta.