Luiz bai da tabbas a Chelsea — Conte

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Luiz ya koma Chelsea daga Paris St-Germain kan kudi kan fam miliyan 34

Kocin Chelsea, Antonio Conte ya ce bai san makomar mai tsaron baya David Luis ba kan ko zai ci gaba da buga tamaula a Stamford Bridge.

Luiz mai shekara 30 bai buga wa Chelsea gasar Premier da ta ci Manchester United 1-0 ba a ranar Lahadi, inda Andreas Christensen ne ya maye gurbinsa.

Conte ya ce ya kamata Luiz ya kara kwazo tukuru, idan ba haka ba zai ci gaba da zama a kan benci.

Kocin ya kara da cewar bai san makomar Luiz ba a Chelsea, amma ya san cewar Christensen shi ne ke kan ganiya a yanzu zai kuma zama gwarzo nan gaba.

Luiz dan kasar Brazil ya buga wa Chelsea wasa uku baya a Premier da karawar da Roma ta doke ta 3-1 a gasar Zakarun Turai.

Conte ya ajiye Luiz a kan benci a fafatawa da United a ranar Lahadi, inda dan kwallon ya rufe kansa da bakin kyalle.

Dan wasan ya koma Stamford Bridge da taka-leda a karo na biyu daga Paris St-Germain kan fam miliyan 34, yana daga cikin 'yan wasan da suka ci wa kungiyar Premier a bara.